Viktor Yanukovych ya ki yin murabus

Shugaban Ukraine Viktor Yanukovych Hakkin mallakar hoto r
Image caption Shugaban Ukraine Viktor Yanukovych

Shugaban Ukraine, Viktor Yanukovych, ya ce ba zai sauka daga kan mukaminsa ba.

A cikin sanarwar da ya bayar ta gidan talabijin daga birnin Kharkiv na gabashin kasar, Mr Yanukovych ya bayyana matakan da masu adawa da shi a majalisar dokoki su ka dauka da cewa, halayya ce ta 'yan banga, kuma juyin mulki ne.

Shugaban ya kwatanta yanayin siyasar da ake ciki a kasar da lokacin da jam'iyyar 'yan Nazi ta soma tashe a Jamus a shekarun 1930.

Viktor Yanukovych ya kuma ce, majalisar dokokin Ukraine din ta keta doka bayan da ta zabi sabon kakaki, sannan kuma ta bada umurnin a saki jagorar 'yan adawa, Yulia Tymoshenko, daga gidan kurkuku nan take.

Shugabannin hukumomin tsaron kasar hudu sun bayyana a majalisar dokoki inda su ka sha alwashin bauta wa jama'ar kasar.

'Yan adawa masu fafutuka sun kame hanyoyin shiga fadar shugaban kasa a Kiev, babban birnin na Ukraine.

Ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov, ya ce 'yan adawa a Ukraine ba su mutunta yarjajeniyar da suka kulla a ranar Juma'a da shugaba Yanukovych ba.

Ya ce, masu tsatsauran ra'ayi da ke dauke da makamai, wadanda kuma ke barazana ga 'yancin Ukraine din, su ne ke jagorantar 'yan adawan.

To sai dai a cewar ministan harkokin wajen Poland, Radoslaw Sikorski, wanda ya shiga tsakani a rikicin, majalisar dokokin Ukraine ba ta saba wa doka ba.

Ya ce, a yanzu ya rage wa shugaba Yanukovych ya rattaba hannu a kan sabon kundin tsarin mulkin kasar don ya zama doka.