An haramta luwadi a Uganda

Uganda Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Yoweri Museveni

Shugaba Yoweri Museveni na Uganda ya sanya hannu akan wata sabuwar doka mai cike da kace- nace data hana yin luwadi.

Dokar ta tanadi hukuncin zaman gidan kurkuku na lokaci mai tsaho ga wadanda suka aikata luwadin.

Shugaban ya sanya hannu ne a gaban Jami'an gwamnati da kuma manema labaru.

A ranar Lahadi ne Shugaba Barack Obama ya ce idan aka zartar da dokar, hakan zai kasance koma baya ga 'yan kasar ta Uganda.