Masar: El-Beblawi ya sauka daga mukamin sa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masar na fuskantar yaje- yajen aikin ma'aikatan gwamnati

Firai Ministan Masar Hazem el-Beblawi da kuma 'yan Majalisar zartarwasa sun sauka daga kan mukamansu babu zato babu tsammani

A wata sanarwa da ya yi wacce aka watsa kai tsaye ta gidan talabijin din Kasar, Mr El-Beblawi ya ce Masar na fuskantar karuwar yaje- yajen aikin ma'aikata a 'yan makonnin da suka gabata.

Ya ce babu wata gwamnati a duniya da zata iya biyan dukkanin bukatun al'ummarta cikin dan kankanin lokaci.

Gwamnatin rikon kwaryar kasar mai samun goyan bayan soji ta kama aiki ne a watan Yulin bara bayan da sojoji suka hanbarar da Shugaba Mohammed Morsi.

Karin bayani