Kotun ICC na nazari kan Boko Haram

Hakkin mallakar hoto youtube
Image caption Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau

Babbar mai shigar da kara ta kotun hukunta manyan laifuka ta duniya-ICC, Fatou Bensouda, ta ce a yanzu haka suna matakin farko na bincike domin gano ko an aikata laifukan take hakkin bil adama a yakin da ake yi da 'yan kungiyar Boko Haram.

Mrs Bensouda ta bayyana haka ne a wani taro da ma'aikatar shari'a tare da hadin gwiwar ofishin mai baiwa shugaban Nigeria shawara kan tsaro suka gudanar a Abuja, kan yadda za a kare hakkin bil adama yayin da ake fafatawa da 'yan kungiyar Boko Haram da suka addabi arewacin kasar.

Dama na kallon Boko Haram a matsayin kungiyar da ta aikata laifukkan yaki.

Haka zalika ana zargin jami'an tsaron kasar da ci zarafin jama'a yayin da suke kokarin murkushe 'yan kungiyar ta Boko Haram.

'Allah-wadai'

Image caption An kashe mutane fiye da 100 a Izge

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya yi Allah-wadai da hare haren baya baya nan da 'yan kungiyar da ake kira boko haram ke kaiwa a Najeriya.

A cikin wata sanarwa da aka aikewa manema labaru Mr Kerry ya ce rikici ne mai tada hankali kuma ba dai dai bane kuma duniya ba za ta amince da shi ba . Shafuka masu alaka

Sakataren harkokin wajen Amurka ya yi alkawarin cewa kasarsa za ta ci gaba da marawa Najeriya baya wajen yaki da kungiyar wadda gwamnati Amurka ta bayana a matsayin 'yan ta'ada.

Tun daga farkon wannan shekarar, kungiyar Boko Haram ta hallaka mutane fiye da 300 a hare-hare da dama a jihar Borno da Adamawa.

Karin bayani