Renzi ya gabatar da manufofinsa ga majalisar dokoki

Matteo Renzi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mr Renzi ya ce tsare-tsaren na da tsauri, amma suna da kyau

Sabon firaministan Italiya Matteo Renzi ya fadawa majalisar dokokin kasar irin shirye-shiryen gwamnatin sa na kawo sauye-sauye gabanin kuri'ar tabbatar da shi akan mukamin sa.

Mr Renzi dai na son kawar da majalisar dattawa daga cikin masu shirya doka, kazalika yana kuma son a tattauna akan batun garanbawul a bangaren haraji da kuma ayyukan kwadago kafin nan da watan Maris mai zuwa.

Sabon Firaministan ya kuma ce yana sane da cewa wadannan tsare-tsare na sa masu tsauri ne, amma kuma ya ce suna da kyau ga al'ummar kasar.

Wadannan sauye-sauye dai na kunshe a cikin yarjejeniyar da suka kulla ta kawo sauyi tare da tsohon firaministan kasar Silvio Berlusconi.

Masu sharhi na ganin Mr Renzi zai iya lashe kuri'ar tabbatar da shi din, sai dai kuma rinjayensa zai iya raguwa bayan wasu daga cikin 'yan jam'iyyarsa sun yi barazanar hana tabbatar da matakan nasa.

Karin bayani