'Abincin da ake baiwa dalibai a Kano ya ragu'

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An koka game da raguwar abincin da gwamnati ke baiwa yara a makarantu

Wasu masu da ruwa da tsaki a harkar makarantun firamare a jihar Kano sun fara nuna damuwa da abin da suka ce raguwar yawan abincin da gwamnatn jihar ke bai wa makarantun don ciyar da yaran da ke karatu.

Gwamnatin dai ta bullo da tsarin ne na bai wa 'yan makarantar abinci da nufin karfafa musu gwiwa da kuma janyo hankalin iyaye wajen kai 'ya'yansu makaranta.

A yanzu dai a mafi yawan makarantun abincin baya isa yadda kowa zai samu.

To sai dai gwamnatin jihar ta ce babu wani abu da ya sauya dangane da yadda ake ba da abincin.

Karin bayani