Jihar Lagos ta hana nuna tsiraici.

Hakkin mallakar hoto AP

Umarnin hana ma'aikata sanya sutura mai nuna tsiraici da gwamnatin jihar Lagos a Nijeriya ta bayar ya soma aiki, da nufin tabbatar da ɗa'a da kuma kare mutunci.

Rahotanni dai na cewa, gwamnatin jihar Lagos din ta dauki wannan mataki ne domin kawo karshen yawaitar sanya sutura mai nuna tsiraici.

Duk da cewa, gwamnati ba ta bayyana wani hukunci ba, amma ta ce, zata dau mataki a kan duk wadanda suka ƙi bin wannan umarni.

A hira da wakilinmu a Lagos wasu sun yaba da wannan mataki, wasu kuma sun ce, ba zai yi wani tasiri ba.