Mozilla zai yi waya mai sauƙin kuɗi

Samfurin sabuwar wayar Mozilla Firefox

Asalin hoton, MOZILLA

Bayanan hoto,

Samfurin sabuwar wayar Mozilla Firefox

Kamfanin Mozilla ya gabatar da wani samfurin wayar salula da za a saya dalar Amurka 25, domin kasashe masu tasowa.

Kamfanin wanda ya yi fice saboda hanyar shiga shafukan internet ta Firefox da ta shahara ya haɗa gwiwa da wani kamfanin China mai suna Spreadtrum.

Shi dai kamfanin Spreadtrum ya na kera matattarar bayanai na waya masu saukin kudi.

Duk da cewa wannan waya ba za ta kasance kamar manyan wayoyi ba, amma za a iya amfani da ita wajen shiga Internet.

Wasu lura da al'amura sun ce, wannan waya za ta samu karbuwa ga masu sayen wayoyi masu matsakaicin farashi.

Wayoyi masu matsakaicin kudi suna samun karbuwa a kasashe masu tasowa saboda, baya ga yin waya kadai, ana yin amfani da da su wajen yin wasu harkokin sadarwa.

Asalin hoton, MOZILLA

Bayanan hoto,

Samfurin wayar Mozilla

Burin kamfanin Mozilla

Fatan kamfanin na Mozilla shi ne ya kame kasuwa a kasashe masu tasowa inda sauran kamfanonin waye ke fatan samun shiga sosai.

Sai dai kuma wannan aniya ta kamfanin na Mozilla za ta fuskanci kalubale daga wasu kamfanonin da suka yi suna sosai.

Kamfanin Mozilla ya ce, wannan waya zata bude wata sabuwar kasuwa.

Dama dai kamfanin Huawei ya yi wasu samfurin waya dake amfani da manhajar Forefox OS Mozilla.

Baya ga ita wannan waya da farashinta zai kasance $25 kamfanin Mozilla ya ƙaddamar da wasu manyan wayoyi tare kamfanonin Huawei da kuma ZTE na China.