An kashe wani kwamanda a Syria

Hakkin mallakar hoto
Image caption Ana kara samun rashin jituwa tsakanin 'yan gwagwarmayar Islama a Syria

Masu fafutuka a Syria sun ce an kashe wani babban kwamandan 'yan tawaye da ke da alaka da kungiyar al-Qaeda a wani harin kunar bakin wake.

Kwamandan kungiyar 'yan gwagwarmayar Islaman mai suna Abu Khaled al-Suri na daga cikin mutane da yawa da aka kashe.

Lokacin da wasu 'yan gwagwarmayar masu adawa da kungiyarsa suka kai farmaki sansanin kungiyar tasa, me suna Ahrar Al-Sham a Aleppo.

Magoya bayan kwamandan sun zargi wata kungiyar ta 'yan gwagwarmaya me suna ISIS a takaice da hannu a kisan shi, amma kungiyar ta musanta hakan.