Masar: Mahlab zai kafa gwamnati

Adly Mansour Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana yunkurin kafa sabuwar gwamnati a Masar

Wata jarida da hukumomi ke gudanar da ita a Masar ta ce ministan gidajen kasar wanda ya sauka daga kan mukaminsa Ibrahim Mahlab ne zai kafa sabuwar gwamnati.

Hakan na faruwa ne bayan murabus din Firai ministan kasar da kuma 'yan majalisar zartarwar sa a ranar Litinin.

Jaridar Al Ahram ta ambato Mr Mahlab yana cewa Shugaban rikon kwaryar Kasar Adly Mansour ne ya bukace shi da ya hau kujerar Firai Ministan Kasar.

Karin bayani