An zargi Erdogan da yunkurin boye kudi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Erdogan na fuskantar binciken cin hanci da rashawa

'Yan adawa a Turkiyya sun yi kira ga Firai Ministan Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya sauka daga kan mukaminsa, bayan wasu zantutukan da ake zargin sun yi shi da dansa sun bayyana shirinsu na boye wasu makuden kudade.

Babbar Jamiyyar adawa ta Republican People's Party tace gwamnati ta rasa kimarta.

Jam'iyyar Nationalist Action Party ta bayyana cewa a gudanar da bincike.

Sai dai Firai Ministan ya yi alla-wadai da bayanan da aka nada da cewa ba gaskiya bane.

Ya kuma ce za a hukunta duk wadanda keda alhakin nadar maganganun.

Mr Erdogan dai na fuskantar binciike game da zargin cin hanci da rashawa wanda yake zargin makarkashiya ce ake masa