'An hana musulmin Rohingya haihuwa'

Sansanin musulmi a Burma Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An hana musulmi yawan haihuwa

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun ce sun sami wasu bayanai dake tabbatar da cewa hukumomin Burma sun aiwatar da wata manufa ta nuna wariya akan tsirarun musulmin Rohingya.

Wata kungiya da ake kira Fortify Rights ta ce gwamnatin jahar Rakhine tana hukunta duk musulmin da ya haifi yara fiye da biyu.

Wani wakilin BBC a Burma ya ce mabiya addinin Bhudda na da fargabar cewa watarana zasu kasance cikin 'yan tsiraru saboda yadda musulmi suke haihuwar 'ya'ya da yawa.

An kiyasta cewa 'yan Rohingya dubu dari takwas ne ke zaune a yammacin Kasar

Karin bayani