Saudiyya za ta kafa cibiyar horon alƙalai

Image caption Abdallah, Sarkin Saudiyya

Hukumomin Saudiyya za su kafa wata cibiyar horas da alƙalan ƙasar domin inganta yadda suke gudanar da aikinsu.

A ciki da wajen Saudiyyar ana kokawa da rashin ƙwarewar alƙalan ƙasar.

Tsarin shari'ar kasar ya baiwa alƙalai ikon yanke hukunci ba tare da dogara da wani tsari tsayayye ba.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun ce, hakan yana kawo sabani hukunci da kuma yin hukunce-hukunce da ake sanyawa ayar tambaya.

'Yan kasuwa dai suna ganin wannan tsari yana kashe gwiwar masu sha'awar zuba jari a kasar.

Amma an jima masu tsaurin ra'ayi suna tirjewa duk wani yunƙurin yin sauyi ga ɓangaren shari'a na ƙasar.