Buni Yadi: An kashe akalla mutane 40

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Abubakar Shekau, jagoran ƙungiyar Boko Haram

A Nijeriya ana ci gaba da samun karin haske dangane da harin da aka kai kwalejin gwamnatin tarayya dake garin Buni Yadi a jihar Yobe.

Wata majiya a asibiti ta ce, mutane akalla 40 ne aka kashe.

Sai dai kuma kakakin gwamnan jihar Yobe, Abdullahi Bego ya ce, mutane 29 aka kashe.

An kashe wasu daliban ne ta hanyar yi musu yankan rago, wasu kuma sun ƙone ƙurmus bayan maharan sun cinnawa makarantar wuta.

Rahotanni na cewa, baki ɗayan makarantar an ƙona ta.

An kai wannan hari ne 'yan sao'i bayan jami'an tsaro dake kusa da makarantar sun janye.

Ana zargin 'yan ƙungiyar Boko Haram ne suka kai wannan hari.

A baya dai ƙungiyar ta sha yin ikirarin cewa, ita ce ta ke kai irin waɗannan hare-hare a makarantu.

Koda cikin watan Satumbar da ya gabata an kashe ɗalibai fiye da 40 a kwalejin koyon aikin gona dake Gujba a jihar ta Yobe.