Goodluck ya soki kisan dalibai a Yobe

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

Shugaban kasar Nigeria Goodluck Jonathan ya bayyana bakin cikinsa da samun mummunan labarin kisan da ya ce yan ta'adda sun yi wa daliban sakandare a jihar Yobe.

Mr Jonathan ya tabbatar wa 'yan kasar cewa gwamnatinsa ba za ta gajiya ba a kokarin da take na kawo karshen ta'addanci a sassan kasar wanda ke haddasa asarar rayukan wadanda ba su ji ba su gani ba.

Tun farko bayan harin da aka kai kwalejin gwamnatin tarayya dake Buni a jihar Yobe gwamnan jihar, Alhaji Ibrahim Gaidam ya buƙaci shugaban kasar ya kara yawan sojan a jihar.

Ranar Talata ne dai gwamnan ya ziyarci makarantar inda aka kashe yara 29, amma wata majiya a asibiti ta ce, yawan wadanda aka kashe sun kai 40.

Ya ce, tunda gwamnatin tarayya ce take riƙe da harkar tsaro ya kamata ta ɗauki mataki da gaske domin kawo ƙarshen rikicin.