'Ba sa ni aka yi na yi murabus' - Benedict

Hakkin mallakar hoto AFP

Paparoma da ya yi murabus, Benedict ya fitar da wata sanarwa, yana musanta cewa, tilasta masa aka yi ya yi murabus saboda badaƙala iri iri a fadar Vatican.

A wasikar da aka wallafa a wani shafin Intanet na Italia, tsohon pamaroman ya ce, ya yi murabus ne bisa raɗin kansa ba tare da matsin lambar kowa ba.

Kafofin yaɗa labarai sun yi ta shaci fadi akan murabus din na sa tun bayan sace wasu muhimman takardu a fadar Vatican a shekara ta 2012.

Takardun da aka sace sun ƙunshi bayanai akan badaƙalar kuɗi a fadar Vatican.