Sanusi ya yi ƙarar Jonathan

Hakkin mallakar hoto getty and reuters

Gwamnan babban bankin Nijeriya da aka dakatar, Malam Sanusi Lamido Sanusi ya shigar da ƙara yana ƙalubalantar dakatar da shi da shugaba Goodluck Jonathan ya yi.

Lauyan Malam Sanusi Lamido Sanusi ya shigar da ƙarar a gaban babbar kotun tarayya dake Abuja.

Ƙarar ta buƙaci, kotu ta hana gwamnati daukar duk wani mataki na aiwatar dakatarwar da aka yi wa Malam Sanusi Lamido Sanusi har sai an kammala shari'ar.

Ya kuma buƙaci kotu ta bada wani umarnin da zai hana gwamnatin tarayya hana shi, ko kawo cikas da nufin hana shi ci gaba da aikinsa na gwamnan babban bankin Nijeriya.

Gwamnan CBN din da aka dakatar ya ce, an ɗau matakin dakatar da shi ne saboda ya tono salwantar wasu kuɗaɗe da ya kamata a ce sun shiga asusun gwamnatin tarayya.

Cikin wannan makon ne dai shugaba Goodluck Jonathan ya ce, ya dakatar da gwamnan babban bankin Nijeriyar ne da nufin bada damar a bincike zargin aikata ba daidai ba.