Matsalar mai ta sake kunnowa a Nigeria

Image caption 'Yan bunburutu na cin karensu ba babbaka

Rahotanni daga Nigeria na nuna cewa ana fuskantar dogayen layukan mai a galibin gidajen man kasar a wasu jahohi ciki har da Abuja babban birnin Kasar.

Wadannan dogayen layukan sun sake bulla ne wasu jahohin kasar tun a makon da ya wuce sakamakon karancin man da hukumomi suka danganta da lalata bututan mai a wasu sassan kasar.

Wannan matsala ta sa yanzu haka 'yan bunburuntu na cin karensu ba babbaka.

Sashen kula da albarkatun man fetur na DPR ya tabbatar wa 'yan Nigeria samun wadatar man, to amma bai ce uffan a kan ko yasuhe za a daina ganin dogayen layukan a gidajen man ba.

Sai dai wani babban jami'in kamfanin mai na NNPC Dr. Umar Farouk ya shaidawa BBC cewa 'yan kasuwa ne suke boye man da gangan da tunanin cewa za'a kara fasahin sa a nan gaba.