Nigeria na bikin cika shekaru 100

Hakkin mallakar hoto nigeria villa
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan ya ce hadewar sassan Nigeria alheri ne.

A ranar Alhamis ne ake fara bikin cikar Nigeria shekara 100 da hadewar lardunanta wuri guda a matsayin dunkulalliyar kasa.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yiwa al'umar kasar jawabi inda ya ce hadewar kasar alheri ne ga al'ummarta.

An dai shirya shagulgula daban-daban, ciki har da lacca da raye-rayen gargajiya.

Ana kuma sa ran shugabannin kasashe da dama za su halarci bikin.

Ranar 1 ga Janairun 1914 ne gwamnatin mulkin mallakar Birtaniya ta hade sassan Arewaci da Kudancin Nigeria zuwa kasa guda.