Putin ya sa a yi atisayen soja kan Ukraine

shugaba Putin na Rasha Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Putin na Rasha

Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya bada umurnin a yi atisayen soja ba zato ba tsammani a dukan fadin yammacin kasar, mai makwabtaka da Ukraine.

Hakan na faruwa yayin da zaman dar-dar ke karuwa, bayan an kawar da shugaban Ukraine, Viktor Yanukovych.

Ma'aikatar tsaron Rashar ta ce, sojoji dubu dari da hamsin ne ke cikin shirin ko ta kwanan.

Rasha ta kuma ce, tana daukar matakan kare jiragen ruwan kasar na yaki da ke tekun Black Sea, a yankin Crimea na Ukraine.

Wani kakakin fadar gwamnatin Amirka yayi kira ga wadanda ya kira: masu shishigi daga waje, a yankin, da su mutunta 'yancin kasar Ukraine, su kuma daina yin kalamai irin na takala.