Gwamnan Yobe ya soki sojin Nigeria

Hakkin mallakar hoto yobe govt
Image caption Gwamna Ibrahim Gaidam ya ce sojoji ba su kai dauki ba bayan sa'o'i biyar da kai harin.

Gwamnan jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Nigeria ya koka da sojin kasar bisa gaza mai da martani kan kisan fiye da dalibai 50 na sakandiren gwamnatin tarayya da ke garin Buni Yadi.

Ya ce, abin takaici ne sa'o'i biyar bayan harin da ake zargin mayakan Boko Haram da kai wa, babu wasu jami'an tsaro da su ka isa garin domin ba da kariya.

Jami'an yankin sun ce an janye sojojin da ke wani shinge tsaro kusa da makarantar daf da lokacin da za a kai harin.

Wakilin BBC da ya je makarantar ya ce baki daya yaran da aka kashe maza ne yayin da maharan su ka umarci dalibai mata da su koma gida, su yi aure, su bar karatu.

Karin bayani