Ɗaliban Yobe sun koka da rashin tsaro

Image caption A watan Satumba na kashe ɗalibai fiye da hamsin a Gujba

Ƙungiyar daliban jihar Yobe ta kasa ta koka game da irin hare-haren da ake kaiwa ɗaliban a makarantun kwana a jihar, kuma tayi kira ga gwamnati ta ɗau matakan samar da tsaro a makarantu.

Harin da aka kai na baya bayan nan a makarantar gwamnatin tarayya da ke garin Buni Yadi a karamar hukumar Gujaba ya yi sanadiyar mutuwar ɗalibai maza 29, da dama kuma sun jikkata.

Shugaban ƙungiyar daliban jihar Yobe ta ƙasa, Comrade Muhammed Aji Baitu Damaturu ya ce, batun tsaro alhakin gwamnatin tarayya ne dan haka ta ta shi tsaye.

Ƙungiyar ɗaliban ta bayyana takaicin ganin yadda ake kashe 'yan makaranta da dama.

Koda a watan Satumbar bara ma 'yan Boko Haram sun kashe ɗalibai fiye da 50 a kwalejin koyon aikin gona dake garin Gujba.