Bankin duniya: Ana asarar abinci a duniya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Miliyoyin mutane a duniya na rasa abincin da zasu ci'

Wani rahoto da bankin duniya ya fitar ya ce ana asarar akalla daya bisa hudu na abincin da duniya ke samarwa.

Bankin ya ce akwai dalilai da dama na asarar abincin.

A arewacin Amurka, laifin daga masu amfani da abincin ne.

A yankin Afirka kudu da sahara ana asarar abinci mai yawa a lokacin samar da shi da kuma sarrafa shi.

Shugaban bankin duniya Jim Yong Kim ya ce irin wannan barnar albarkatun abinci abin kunya ne a lokacin da miliyoyin mutane ke kwanciya ba tare da sun samu abinda zasu sa a bakinsu ba.

Rahotan ya ce hanyoyin da za a magance wannan matsala sun hada da inganta ayyukan gona da kuma zuba jari a harkar sufuri da kuma wuraren adana abincin.