Tsaro: Faransa za ta tallafawa Nijeriya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Francois Hollande, shugaban Faransa

Shugaban Faransa, Francois Hollande ya ce, ƙasarsa zata tallafawa Nijeriya a yaƙin da ta ke yi da ƙungiyar Boko Haram,

Ya ce, Faransa a shirye ta ke ta tallafa wajen yaƙi da tsatsauran ra'ayi.

Shugaba Hollande ya bayyana takaici dangane da ayukan kungiyar Boko Haram, inda ya ce, kisan dalibai a jihar Yobe abin Allah-wadai ne.

Ya kuma ce, Faransa za ta goyi bayan Nijeriya wajen ƙarfafa dimikradiyya, yana mai cewa, yaƙi da tsatsauran ra'ayi tamkar ƙarfafa dimukradiyya ne.

Shugaba Hollande ya bayyana wannan ne a Abuja a matsayinsa na baƙo na musamman a taron cikar Nijeriya shekaru 100 da zama kasa guda.

Ana kuma sa ran shugaba Goodluck Jonathan da Shugaba Hollande zasu tattauna batutuwan kasuwanci da kuma zuba jari.