Boko Haram: Sojoji sun zafafa kai farmaki

Hakkin mallakar hoto AFP

Rundunar sojan Nigeria ta ce, ta zafafa kai farmaki a kan 'yan kungiyar Boko Haram kuma dan haka ne ma 'yan kungiyar suka takura suke kai wa kauyuka da makarantu hari.

A wata sanarwa da hedikwar tsaron Najeriyar ta fitar, ta kuma ce, tana ci gaba da farautar 'yan Boko Haram din a jihohin Adamawa, da Borno, da kuma Yobe inda cikin 'yan makonnin nan 'yan kungiyar suka kashe mutane fiye da dari uku.

Dakarun Najeriyar sun ce, yanzu sun ɗaga matsayin yaƙin da su ke yi da ƙungiyar Boko Haram.

Sun kuma ce, 'yan Boko Haram suna aukawa ƙauyuka da garuruwa ne domin kwasar kayan abinci da fasa bankuna domin kwasar kuɗi.

Hedikwatar dakarun Nijeriyar ta kuma ce, 'yan Boko Haram da suka kai hari a Buni Yadi sune suke ci gaba da kai hare-hare a jihar Adamawa a ƙokƙarinsu na tserewa.

Sanarwar ta kuma ce, 'yan Boko Haram suna ƙoƙari ne su tsallaka Kamaru,

Sojan Nijeriyar sun ce, sun kashe 'yan Boko Haram shida, kuma sun kama biyu, amma an kashe daya.