Doha: Mutane 12 sun halaka a gidan abinci

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Cikin wadanda suka mutu har da kananan yara

Jami'ai a Qatar sun ce mutane 12 sun mutu, sannan 30 sun jikkata bayan abinda suka ce fashewar tukunyar iskar gas a babban birnin kasar Doha

Fashewar ta auku ne a wani gidan cin abinci na Turkiyya dake wajen wani katafaren kantin saida kayayyaki a Doha.

Fashewar mai karfi dai ta janyo rushewar wani bangaren ginin, da kuma lalata motocin dake kusa da wajen

An bada rahotan mutuwar kananan yara biyu cikin wadanda aka kashe.

A watan Mayun shekarar 2012, wata wuta data tashi a wani rukunin shaguna a Doha ta kashe mutane 19 da suka hada da kananan yara.