Rasha ta gargadi NATO a kan Ukraine

Shugaba Putin na Rasha Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Putin na Rasha

Rasha ta ce a shirye take ta yi aiki tare da kasashen yammacin duniya a kan kaucewa wani rikici a Ukraine, to amma ta gargadi kungiyar tsaro ta NATO game da yanke shawarar a madadin jama'ar Ukraine.

Wani kakakin ma'aikatar harkokin wajen Rasha Alexander Lukashevich, ya ce dole ne duk wani mataki ya yi la'akari da bukatun 'yan kasar Ukraine baki daya, hade da 'yan kasar masu magana da harshen Rashanci masu yawa , amma kuma tsiraru.

Sabon Pirayim Ministan wucin gadi na Ukraine ya soki hambararren Shugaban kasar Viktor Yanukovych da kuma gwamnatinsa da zazzage aljifan gwamnati karkaf.

Arseniy Yatsenyuk ya shedawa majalisar dokoki cewar an kwashe biliyoyin daloli zuwa wasu asusan ajiya a wasu kasashen ketare a cikin shekaru 3n da suka wuce.

A halin da ake ciki kuma, hukumomin na Ukraine sun nemi taimakon kudi daga hukumar lamuni ta duniya -IMF, kuma Switzerland ta ce a shirye take ta kwace duk wasu kudin da Mr Yanukovych keda su a Bankunanta.

Karin bayani