'West Brom na cikin mawuyacin hali'

Hakkin mallakar hoto
Image caption Ana nuna damuwa game da salon wasan Pepe Mel

Kulab din West Brom ya gudanar da tattaunawa game da gazawar kulab din tare da bayyana cewa Manaja Pepe Mel wanda ke fuskantar matsin lamba zai taimaka wajen kaucewa fadawa relegation.

Mel dan shekaru 50 bai yi nasara a wasanni shidan da ya yi ba tun daga lokacin da ya karbi ragamar kulab din, abinda ya sa ake ta rade radin cewa za a kore shi daga aikinsa.

Manyan ‘yan wasa sun nuna damuwa game da salon wasan sa, yayinda kulab din ke kokawar ci gaba da kasancewa a Premier League.