Aku ta fallasa kisan kai a India

Hakkin mallakar hoto Frank Wouters
Image caption Akun na ta da hankalinta idan aka ambaci sunan mai kisan.

Wata aku a garin Agra da ke arewacin India ta taimaka wa 'yan sanda wurin kama wanda ya kashe uwargijiyarta.

Bayan mutuwar matar, akun mai suna Heera kan fututttuke ta tada hankalinta duk lokacin da dan marigayiyar ya shigo gidan ko kuma aka ambaci sunansa.

Iyalan marigayiyar sun rinka ambatar sunayen dangi da makwabta akun ba ta motsa ba amma da zarar sun ambace sunansa sai ta rikice.

Ranar Talata ne aka kama matashin da abokin burminsa bayan da 'yan sanda suka samu addar da ya kashe gwaggon ta sa da kuma sarkokinta na zinariya a wajensa.

'Yan sanda kuma sun ce ya amsa laifin shi ne ya kashe matar.