Shuwa: Gwamna Nyako ya sha da kyar

Image caption Gwamnan Adamawa ya ranta ana kare a Shuwa

Rahotanni daga Shuwa a jahar Adawama arewacin Nigeria na cewa Gwamnan jahar Adamawa Murtala Nyako tare da mukarrabansa sun ranta ana kare bayan da aka soma harbe- harben bindigogi yayin wata ziyarar jaje da gwamnan ya kaiwa mazauna garin.

Mai magana da yawun gwamnan jahar Adamawa Ahmad Sajo shine ya shaidawa BBC wannan labari.

Ahmad Sajo ya ce "Mun je Shuwa da Gwamna mun jajantawa na Shuwa, muna shirin zuwa Michika sai muka ji harbin bindigogi. Haka jami'an tsaro suka saci Gwamna suka sashi a wata motar da ba tashi ba. Haka muka kama hanya da gudu muka bar wannan wurin. Abin dai ba a cewa komai".

Yawan mutanen da aka kashe a garin Michika da Shuwa dake jihar Adamawa a yankin arewa maso gabashin Nigeria ya kai akalla mutane 28.

Sojojin Nigeria dai sun bayyana cewa sun zafafa farmakin da suke kaiwa 'yan Kungiyar Boko Haram.