An dakatar da bashin Uganda saboda luwadi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan luwadi da madigo za su fuskanci daurin rai da rai.

Bankin duniya ya dakatar da wani rancen $90miliyan ga Uganda, kwanaki kadan bayan da shugaban kasar Yoweri Museveni ya rattaba hannu a dokar haramta luwadi da madigo.

Bankin ya ce zai yi nazari domin tabbatar da cewar sabuwar dokar ba za ta iya illa ga manufar habaka kiwon lafiya a Uganda, wacce saboda ita za a ba da bashin ba.

Dokar da shugaba Museveni ya sa hannu ranar Litinin ta tsananta hukuncin da gwamnatin Uganda za ta iya yi wa 'yan luwadi da madigo.

Dokar na shan suka daga kasashen yammacin Turai, inda Denmark da Norway su ka ce za su janye tallaffi daga gwamnati zuwa kungiyoyin ci gaban al'umma.