Ukraine: Yanukovych ya ce har yanzu shine Shugaba

Victor Yanukovych

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Victor Yanukovych

Shugaban Ukraine da aka hambarar, Viktor Yanukovych, ya yi wani taron manema labarai yau a birnin Rostovon-Don na Rasha, kusa da kan iyaka da Ukraine din.

Mr Yanukovych ya ce dole ta sa ya bar kasarsa saboda ana yin barazana ga rayuwarsa.

Ya kuma kara da cewa dole a awaitar da yarjajeniyar da aka kulla a makon jiya, idan har ana son a shawo karshen rikicin.

Sai dai ya kara da cewar ba zai bukaci Rasha ta mayar da shi kan karagar mulki ba.

A birnin Kiev, babban birnin Ukraine, gwamnatin wucin gadi ta zargi Rasha da mamaye kasar, bayan da wadanda ta ce mayakan ruwan Rasha ne da ke tekun Black Sea, suka killace filin jirgin saman Sevastopol, a yankin Crimea.