Ukraine: Yanukovych ya fito daga buya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Yanukovych ya ce a shirye yake ya yi gwagwarmaya kan makomar Ukraine,

Hambararren Shugaban Ukraine Viktor Yanukovych ya bayyana a fili a karon farko tun lokacin da zakara ya ba shi sa'a ya arce ya bar Kiev a karshen mako.

A wajen wani taron manema labarai a birnin Rostov -on -Don dake kudancin Rasha kusa da kan iyaka da Ukraine, ya ce, wasu da ya kira matasa masu kishin kasa da neman fitina 'yan kalilan a cikin al'umar Ukraine sun kore shi daga kan mulki ba kan ka'ida ba.

Ya ce, babu wanda ya hambarar da shi. 'An tilasta mani barin Ukraine, tare da barazana a rayuwa ta da ta mutanen da ke kusa da ni'.

Mr Yanukovych ya ce ya zaku , kuma a shirye yake ya yi gwagwarmaya kan makomar Ukraine, a kan abinda ya kira ta'addancin wadanda a halin yanzu ke kokarin mulkar kasar.

Karin bayani