'Yan gudun hijirar jamhuriyar tsakiyar Afirka a Chadi na ciki mummunan hali

'Yan gudun hijirar Jamhuriyar tsakiyar Afrika  Hakkin mallakar hoto c
Image caption 'Yan gudun hijirar Jamhuriyar tsakiyar Afrika

Kungiyar likitoci ta Medecins Sans Frontieres ta yi gargadi da babbar muryar, kan mummunan halin da 'yan gudun hijirar da ke tserewa daga jamhuriyar tsakiyar Afirka ke ciki.

Wani likita a sansanin 'yan gudun hijirar Sido da ke makwabciyar kasar Chadi, inda mutane dubu goma sha ukku ke zaune, ya ce kusan rabin marasa lafiyar da yake dubawa, suna fama da yunwa.

Wani likitan kuma ya ce akwai yaran da ke isa sansanin da ciwo a ka, bayan an sare su da adduna.

Kungiyar ta Medecins Sans Frontieres ta ce, akwai mata dayawa da dole ta sa suka shiga karuwanci, don dai su samu su ciyar da 'ya'yansu.

Rikicin addini ya barke ne a jamhuriyar tsakiyar Afirkar, bayan juyin mulkin da aka yi a kasar, a watan Maris na bara.