Borno: Farmakin soji ya halaka mutane

Hakkin mallakar hoto AFP

Rahotanni daga Najeriya sun ce wani farmaki da sojin saman kasar su ka yi niyyar kaima 'yan bindiga a Jihar Borno ya halaka fararen hula da dama.

An kai harin ne a kauyen Ndagu na Karamar Hukumar Askira Uba dake kudancin jihar.

Dan majalisar dattawan kasar mai wakiltar yankin, Sanata Mohammed Ali Ndume, ya gaya wa BBC cewa an kashe fararen hula biyar an kuma jima wasu da dama raunuka a sabilin harin.

Ya ce sojojin sun jefa bama-bamai ne a kauyen bisa kuskure.

Ya ce sojojin na kokarin kai harin ne akan 'yan bindiga, su ka yi kuskure suka kashe fararen hulan.

Mazauna kauyen dai sun gaya wa BBC cewa a daren jiya ne wani jirgin sama ya jefa bama-bamai a kauyen.

Daya daga cikin wadanda suka ji rauni ya ce an dauko su an kaisu asibiti a garin Mubi dake Jihar Adamawa, mai makwabtaka da Jihar Bornon.

Ya yi ikirarin cewa yawan wadanda aka kashe a harin sun kai 20 yayin da aka ji wa 25 raunuka.

Sai dai rundunar sojin kasar ba ta ce komai ba akan lamarin.

Karin bayani