Obama ya gargadi Rasha

Shugaba Obama Hakkin mallakar hoto
Image caption Rasha ta bayyana cewa sinitirin da sojojin kasar ta ke yi a Ukraine na daga cikin yarjejeniyar da ke tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Obama ya gargadi Rasha da cewar ba za ta sabu ba idan sojoji suka shiga rikicin Ukraine.

Da yake jawabi a fadar White House shugaba Obama yace ya na cikin matukar damuwa game da bayanan da ke nuna cewa sojojin Rasha na shawagi a cikin Ukraine.

Shugaba Obama ya kara da cewa duk wani keta hurumin Ukraine zai kawo matsala sosai, ya kuma yabawa gwamnatin Ukraine da abin da ya kira kokarin kwantar da hankali.

Sai dai jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya Vitali Churkin yace duk wani shige da ficen Sojin Rasha a Ukraine na daga cikin jarjejeniyar da ke tsakanin kasashen biyu.

Karin bayani