An kashe mutane 29 a China

Tashar jirgin kasa
Image caption Tashar jiragen kasa a yankin Kunming na China

Wani gungun mutane dake rike da wukake sun kashe mutane akala 29 yayinda wasu sun ji raunuka a wata tashar jiragen kasa a yankin kudu maso yammacin Kunming dake China.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce maharan , dake sanye da bakaken tufafi, sun far wa fasinjoji da suka layi domin siyan tikiti , inda suka yanka ko dabawa wadanda suka yi kokarin tserewa wuka.

Kamfanin dilancin labaru na Xinhau ya ce 'yan sanda sun harbe akala hudu daga cikin maharan.

An dai kama wata mata da ake zargin tana da hanu a cikin harin.

Kawo yanzu mahukunta kasar na ci gaba da farautar neman maharan.