'Yan bindiga sun kai hari a Mainok

A Najeriya wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne sun kai sabon hari a daren jiya a kauyen Mainok da ke Jihar Borno.

Mazauna garin sun ce an kashe fiye da mutane 30, an jima wasu raunuka, an kuma kone gidaje da dama.

Wani wanda ya tsira daga harin ya ce 'yan bindigar sun shiga kauyen ne sanye da kayan soji, su ka bude wa jama'a wuta da manyan bindigogi.

Kauyen ya fuskaci hare haren 'yan bindiga a watannin baya.

Hukumomi ba su ce komai ba game da wannan farmaki.

An kai harin na Mainok din ne jim kadan bayan tashi wasu bama-bamai a Maiduguri, fadar gwamnatin Jihar Borno, wadanda su ka halaka fiye da mutane 50.

Wani jami'in kungiyar agaji ta Red Cross ya ce akalla mutane 51 ne aka kashe a hare-haren na Maiduguri.

Karin bayani