An yi jana'izar mutane 47 a Mainok

An yi jana'izar mutane 47 da 'yan bindiga su ka kashe a kauyen Mainok dake Jihar Borno a Najeriya.

'Yan bindigar, wadanda ake zaton 'yan Boko Haram ne, sun kai hari a kauyen ne ran Asabar da dare jim kadan bayan wasu bama-bamai sun fashe a Maiduguri, fadar gwamnatin Jihar Bornon, sun kashe mutane five da 50.

Wani jami'in kungiyar agaji ta Red Cross ya ce akalla mutane 51 ne aka kashe a hare-haren na Maiduguri.

Mazauna kauyen Mainok kuwa sun ce fiye da mutane 47 aka kashe a harin da aka kai ma kauyen.

Ranar Lahadi da rana ne aka yi jana'izar mutanen aka kashen.

Wani wanda ya tsira daga harin ya ce 'yan bindigar sun shiga kauyen ne sanye da kayan soji, su ka bude wa jama'a wuta da manyan bindigogi.

Kauyen ya fuskaci hare haren 'yan bindiga a watannin baya.

Jami'an tsaro dai ba su ce komai ba game da farmakin da aka kaima Mainok.

Amma babban jimi'in Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa, wato NEMA, Muhammadu Kanar, ya gaya wa BBC cewa hukumar na agaza wa 'yan Mainok din da abin ya rutsa da su.

Ya kuma ce hukumar na ci gaba da tallafa wa mutanen da harin bama-bamai a Maiduguri ya rutsa da su a ranar Asabar.

Karin bayani