Cocin Anglican ya fitar da ƙa'idoji a Nijeriya

Hakkin mallakar hoto nig anglican church
Image caption Nicholas Okoh, shugaban cocin Anglican a Nijeriya

Reshen Nijeriya na cocin Anglican ya fitar da ƙa'idar cewa, duk waɗanda za su rike muƙami a cocin sai sun yi rantsuwa da Allah cewar, ba za su yi luwaɗi ko maɗigo ba.

Cocin ya ce masu irin waɗannan ɗabi'u na bukatar a yi musu wa'azi kuma ba za su ta taɓa barin irinsu su riƙe kowane muƙami ba a cocin.

A jiya ma dai sai da wasu jam'ian cocin da aka ƙaddamar a Abuja suka yi rantsuwar cewa ba sa yin luwaɗi ko Maɗigo, kuma suka yi tir da ɗabia'ar kafin a naɗa su.

Shugabannin cocin a Nijeriya sun faɗawa BBC cewa, hana masu luwaɗi da maɗigo riƙe muƙamai mataki ne na kare maganar Allah.

Dama wannan batu a baya ya kawo rarrabuwar kawuna tsakanin mabiya cocin a Afirka da kuma na Turai da Amurka.

Wasu ƙasashen Afirka da suka hada da Nijeriya da Uganda sun zartar da dokokin haramta luwadi da madigo.