An sace wani dan Majalisa a Bauchi

Jihar Bauchi
Image caption Jihar Bauchi

Rahotani sun ce ‘yan-bindigar da ba a san ko su wane ne ba, sun sace dan Majalisar Dokokin jihar ta Bauchi mai wakiltar mazabar Lame dake karamar hukumar Toro ne, bayan sallar Magariba, a cikin wani masallacin dake kofar gidansa .

Rahotanin sun ce bayan da 'yan bindigar suka yi awon gaba dan majalisa, Hon Yusuf Nuhu, nan da nan jami’an tsaro da wasu masu sa kai, sun bi ‘yan bindigar inda suka danna har zuwa kan iyakar jihohin Bauchi da Kaduna .

Haka kuma rahotanin sun ce a nan ne 'yan bindigar suka yi watsi da motarsu da wasu kayakinsu kana suka sabi dan majalisar a hannu suka shiga daji da shi sakamakon matsin lamba,

Dan majalisar dokokin jihar ta Bauchi daga ‘yankin na Lame dai shi ne mutum na biyar da ‘yan-bindiga suka sace a jihar cikin kimanin makwanni biyu,