Bill Gates ya fi kowa kuɗi a duniya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Bill Gates, ya fi kowa kudi a duniya

Hamshaƙin attajirin nan, Bill Gates ya sake karɓe kambun kasancewa wanda ya fi kowa kudi a duniya, inji mujallar Forbes.

Yanzu an tantance cewa, Bill Gates ya mallaki kudi dalar Amurka biliyan 76.

Wannan dai na nufin yanzu ya shiga gaban hamshakin attajirin nan dan Mexico, Carlos Slim, wanda yanzu ya koma matsayin mutum na biyu mafi arziki a duniya.

Jimulla akwai mutanen da suke da kudin da ya haura dala biliyan a duniya su 1,645, inji mujallar ta Forbes.

Yanzu dai mutum ba zai shiga sahun mutane 20 mafiya kudi a duniya ba sai yana da kudin da ya kai dalar Amurka biliyan 31.

Bill Gates dai ya shafe shekaru 20 yana cikin mutane 15 mafiya kudi a duniya.