Mun kashe 'yan Boko Haram da dama - Soji

Wasu 'yan sandan Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sai dai babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da ikirarin rundunar sojin Najeriyar

Rundunar sojin Najeriya ta yi ikirarin kashe 'yan kungiyar nan da ake kira Boko Haram da dama, a samamen da ta kai a yankunan Daggu da Yazzu na jihar Borno.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da rundunar ta fitar, inda ta ce sojoji sun shiga yankunan bayan hare-hare ta jiragen sama da aka kai yankunan a karshen mako.

Sanarwar ta kuma ce sojoji ma sun mutu, amma bata bayyana yawansu ba.

Haka kuma rundunar sojin ta musanta kashe fararen hula, a hare-haren da ta kai ta sama.

Wasu masu sharhi a kasar na ganin hare - hare ta saman da sojojin suka kai, a sansanonin 'yan kungiyar Boko Haram da ke dajin Sambisa ne ya janyo karin hare-haren da 'yan kungiyar suka kai kan wasu kauyuka da garuruwan wasu jihohin a arewa-maso-gabashin kasar.