Yahudawa sun bijire wa Isra'ila

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan gargajiyar yahudawan sun ce addininsu ya hana su aikin soji

Dubban 'yan gargajiyar yahudawa sun yi zanga zanga a Isra'ila kan shirin gwamnati na sanya su a aikin soji.

Tarin yahudawan, mazansu da matansu hadi da kananan yara ne su ka zo daga sassan kasar daban daban domin yin addu'oi a birnin Kudus, inda kuma suka rike wasu alamu da ke dauke da rubutun cewa ,''ba za mu shiga soja.''

Bisa dokokin Isra'ila ana bukatar yahudawan da ba ruwansu da sha'anin addini su yi aikin soji a kasar.

Zanga zangar dai ta kawo cikas sosai ga harkoki a birnin na kudus, inda ta kai har an rufe manyan titunan birnin da kuma babban titun Isra'ila na shiga birnin.