Ana neman ma'aikacin Polio da aka sace

Hakkin mallakar hoto AFP

'Yan sanda a jihar Bauchi dake arewacin Nijeriya suna ci gaba da neman wani ma'aikacin bada cutar shan inna da wasu 'yan bindiga suka sace jiya a garin Darazo.

Tun farko dai ma'aikatan Polio uku aka sace a Darazo din, amma ya zuwa yanzu an samo biyu daga cikinsu.

Ma'ikatan riga kafin da aka sace tun farko sun hada da mace daya da kuma maza biyu.

Rundunar 'yan sandan jihar ta Bauchi ta ce ta na kokarin gano wadanda suka sace ma'aikatan na kiwon lafiya da nufin kama su.

Ko a watan jiya dai wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun sace wani dan-siyasa, Alhaji Sama'ila Ahamad Illali a garin na Darazo.

Bara ma 'yan-bindiga sun kashe ma'aikatan rigakafin shan-Inna kamar tara a jihar Kano.

Nijeriya da Pakistan da kuma Afghanistan ne kadai kasashen dake fama da cutar shan inna yanzu a duniya.