Maciji ya hadiye kada a Australia

gamsheka Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kasar Australia dai na da macizai

Wata mesa ta haɗiye wani kada, bayan shafe sa'oi da dama suna gumurzu, a gefen wani tafki a Queensland a Australia.

Mutane sun yi dandazo a lokacin da macijin mai tsawon mita uku, ke kokawar haɗiye kadan.

An ɗauki hoton al'amarin a wayar komai da ruwanka, inda macijin ya kanannaɗe kadan.

Daga bisani dai gamshekar ta samu nasarar hadiye kadan, inda ake ganin alamunsa a cikinta.