Dubbai sun cigaba da zanga zanga a Venezuela

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga zangar sun kara da 'yan sandan kwantar da tarzoma

A Venezuela sama da masu zanga zangar adawa da gwamnati dubu daya ne suka yi tattaki a titunan babban birnin kasar, Caracas, a cigaba da zanga zangar da suke yi ta bijire wa gwamnati.

A karshen tattakin masu rajin kawo sauyi sun yi dauki ba dadi da 'yan sanda a unguwannin masu hannu da shuni na Callao da Altamira.

Shugaban kasar Nicolas Maduro ya kara wa'adin hutun bikin al'adun gargajiya na kasar har zuwa karshen mako, inda ya bukaci 'yan kasar da su huta kuma su yi bikin cikin lumana.

Sai dai su kuma a nasu bangaren 'yan adawa sun lashi takobin cigaba da zanga zangar adawa da manufofin gwamnati na tattalin arziki da kuma kama tarin masu zanga zanga da ta yi a watan da ya wuce.