An kai hari garin Jakana dake Borno

Jami'an tsaron Najeriya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jami'an tsaron Najeriya

Rahotanni daga jihar Borno na cewa wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton' ya'yan kungiyar nan da ake kira Boko haram sun kai wa garin Jakana hari a daren jiya.

Jakana gari ne dake da nisan kilomita 33 daga Maiduguri, kuma yana makwabtaka da garin Mainok da 'yan kungiyar ta Boko haram suka kaiwa hari a baya bayan nan abin da ya janyo asarar rayuka da dama.

Rahotanin sun ce an samu asarar rayuka da dama kuma an kona gidaje da dama.

'Yan kungiyar sun kara kaimi wajen kai hare-hare a yankin arewa-maso-gabashin Najeriya a 'yan kwanakin nan.