Dubban mutane sun fice daga Magumeri

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jama'a da dama suna cikin firgici a jihar Borno

Rahotanni na cewa, jita-jitar cewa, 'yan kungiyar Boko Haram za su kai hari garin Magumeri dake jihar Borno a arewacin Nijeriya ta sa kusan kashi uku bisa huɗu na jama'ar garin sun gudu.

Wani mazaunin garin ya fadawa BBC cewa, anyi ta yada jita-jitar cewa, 'yan Boko Haram zasu kawo hari da maraice.

Yanzu haka dai rahotanni na cewa, yawancin wadanda suka rage a garin ba su da halin ficewa ne.

Magumeri dai gari ne da ke da nisan kilomita kimanin 45 tsakaninsa da Maiduguri.

Koda a daren jiya ma dai an kai hari garin Jakana inda aka halaka mutane 11.