Maiduguri: Ana rayuwa cikin fargaba

Hakkin mallakar hoto AP

Wasu mazauna Maiduguri babban birnin jihar Borno sun ce, yanzu haka suna rayuwa cikin fargaba saboda yadda hare-haren Boko Haram ke ƙaruwa a kewayen birnin.

Daga Juma'ar da ta gabata zuwa yau an kashe mutane fiye da 130 a jihar Borno.

Wasu mazauna Maidugurin sun ce, suna kwana ne ido biyu saboda fargabar abinda ka iya faruwa da su.

Wasu rahotanni kuma na cewa, ana samun tururuwar mutane daga kauyuka zuwa cikin Maiduguri sakamakon hare-haren dake faruwa a kauyuka.

Koda a daren jiya an kai harin da ya hallaka mutane dama a garin Jakana dake kusa da Maiduguri.

Kuma wannan ta faru ne bayan kashe jama'a da dama a kauyen Mainok.